Algus a kayan sayarwan da aka yi ya...

Egypt's Dar Al-Ifta

Algus a kayan sayarwan da aka yi yarjejeniyan saye.

Tambaya

Mene ne hukuncin yin algus a cikin kayan sayarwan da akayi yarjejeniyar shigowa da su a tsarin munakasat?

Amsa

Shi algus a cikin kayan sayarwa da aka yi yarjejeniya akai a tsarin munakasat ko makamancin haka to haramun ne a shari’ance, da kuma cin dukiyar mutane da barna, hakika Musulunci ya haramta algus da yodara, sai Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Duk wanda ya ha’incemu to ba ya kan tafarkinmu) Muslim.

An umurci muminai da yin gaskiya kuma su kasance tare da masu gaskiya, Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani kuji tsoron Allah sannan ku kasance tare da masu gaskiya) [At-Tauba:119]

Musulunci ya yi umurni da cika alkawari tare da sharuda a wurin kulla ciniki, sai Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Su Musulmai suna tafiya ne akan sharudansu, sai dai fa sharadin da ya haramta halal ko ya halasta haram) Ad-Daar kutny.

Allah Ta’ala ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas