Kokwanto akan abin da akayi bakacen rantsuwa akansa.
Tambaya
Wani mutum ne ya yi bakacen rantsuwa sannan ya yi kokwanto kan abin da ya yi rantsuwa akansa, mene ne hukuncisa?
Amsa
Duk wanda ya yi bakace sannan ya yi kokwanto ko ya manta nau’in abin da yayi bakace akansa, shin sallah ne ko azumi ko sadaka ko wani abu daban, to anan zai yi kokari ne har ya samu matsaya akan abin da ya fi kwanciya masa a rai sai ya aikata, idan ya yi kokarin bakace amma bai iya gane nau’in bakacensa ba to kaffaran rantsuwa ta kama shi, saboda kokwanto a rantuwar bakace kamar rashin ambatonsa ne, saboda gazawarsa wurin iyakance nau’insa yazo daidai da wanda ya yi bakacen abin da ya kasa cikawa,
Allah Madaukakin Sarki ne mafi sani.