Rikon wanda ba a san asalinsa ba.
Tambaya
Ta yaya shari'a ta kwadaitar da rikon wadanda ba a san asalinsu ba, kuma wani rin lada ake samu akan haka?
Amsa
Idan wasu iyalai suka raini yaro maraya wanda aka san asalinsa wanda ba a yi wasicci da yin hakan ba, ko kuma yaron da ba a san asalinsa ba, domin ya taso tare da yaran gidan, inda zai rabauta da kulawa da ciyarwa kamar kowa a cikin gidan, sakamakon rashin da ya yi na iyaye, to wannan wani aiki ne na alheri mai matukar kyau ga kananan yaran da suka rasa iyayensu, hakan zai katangesu daga daidaicewa, tare da fatan ganin sun taso a matsayin yara salihai nagari a cikin al'umma, har ta kai ga an amfana da su.