Yi wa shugaban ƙungiyar ta’addanci ta ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) mubaya’a
Tambaya
Shin da gaske ne yi wa shugaban ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) mubaya’a wajibi a shari’ance?
Amsa
Lallai yi wa shugaban ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) mubaya’a abu ne da bai halatta ba, ba kuma dole ba ne, hasali ma bai halatta a kira hakan sunan mubaya’a ba; saboda ita mubaya’a ta Musulunci ba ta yiwuwa sai an sami wasu sharuɗɗa da shi shugaban dole ne ya cika su, muhimman waɗannan sharuɗɗa sun haɗa da: Adalci da dukan gamammun sharuɗɗansa (ma’ana dole ne mai shi ya zama an san shi da tarihi mai kyau). A nan kuma an yi matuƙar jahiltarsa, ba a san tarihin shugaban ISIS ba, hasali ma babu wanda ya san sunansa na haƙiƙa, to kuwa ta yaya zai zama shugaban Musulmai. Haka ma a cikin manufofin yin mubaya’a ga shugaba akwai: buƙatar ya zama ya san ilmomin da za su taimaka masa wajen gabatar da ayyukan wajibai da suka hau kansa, waɗanda za su tabbatar da maslahar mutane, kuma ya zama kowa ya san haka, ta yaya mutane za su san haka a tare da mutumin da mutane ba sun san halinsa da iliminsa da kuma ƙwarewarsa ba, wannan kawai ya isa ya lalata wannan mubaya’ar a shari’ance.