Muslimina da ƙungiyoyin ta’addanci ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Muslimina da ƙungiyoyin ta’addanci da ƙungiyar Hawarijawan zamani

Tambaya

Mene ya sanya ake ɗaukan ƙungiyar Ikhwanul Muslimina a matsayin uwar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kuma uwa ga Hawarijawan zamani?

Amsa

Ta ɓangaren tunanin bai ɗaya, ko ta fuskar yin nazari ana la’akari ne da fahimtar wanda  ya assasa ƙungiyar wato Hassan al- Banna, da kuma littafan Sayyid Ƙuɗub wanda ya guntsa daga al-Banna da al-Maududi, fahimtar waɗannan na daga cikin al’amura da suke yi wa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda jagaora a gabashi da yammaci, musamman ma littafan nan guda Biyu wato: “Ma’alim fiɗ – Ɗariƙ”, da kuma “Fi Zilalil Ƙur’an”, ana kallon Hasan al-Banna da Sayyid Ƙuɗub a matsayin iyayen gijin waɗancan ƙungiyoyin a tarihinsu na wannan lokacin.

Amma ta fuskar tarihi, lallai ayyukan ta’addancin da ƙungiyar ‘yan’uwa ta ‘yan ta’adda suka yi shi ne laifin ta’addanci na farko da aka yi a wannan lokacin, a cikin shekarun 1940 na ƙarnin da ya gabata sun kashe firaministoci har guda biyu (2), da wani mai shari’a.

A shekarar 1950 kuwa sun yi ƙoƙarin kashe marigayi shugaban ƙasa Jamal Abdul –Naseer, kuma sun kusa yin nasara akan hakan, sannan suna da hannu dumu- dumu wurin kashe marigayi Muhammad Anwar As-sadaat.

Kuma idan aka lura za a ga da yawan waɗanda suka kafa ƙungiyoyin ta’addanci da mambobinsu suna da alaƙa mai ƙarfi da ƙungiyar ta’addanci na ‘yan’uwa, misali Shukry Mustapha wanda ya kafa ƙungiyar (At-takfir wal hijra), ya kasance suruki ne ga ɗaya daga cikin ‘yan wannan ƙungiyar ta ‘yan’uwa, an kama shi ne a shekarar 1965, tare da waɗanda aka kama su cikin ‘yan ƙungiyar ‘yan’uwa. Wannan duk ya kasance ne kafin ma ya kafa tasa ƙungiyar.

Share this:

Related Fatwas