Hanyoyin da kungiyoyin ‘yan ta’’ada...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hanyoyin da kungiyoyin ‘yan ta’’ada ke bi wurin horar da mabiyansu

Tambaya

Wa su hanyoyi ne mafiya muhimmanci da ‘yan ta’adda ke bi wurin horar da mabiyansu?

Amsa

Ana la’akari da hanyar rudar wasu mata da kuma karkatar da tunaninsu a matsayin muhimmiyar hanya wurin horar da matane domin nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda da kuma shiga kungiyoyinsu,wanda hakan na taimakawa sosai wurin jan ra’ayin mutane zuwa garesu, idan muka kalli kungiyar ISIS zamu ga yanda suke yawaita yin “Auren jihadi” wanda hakan ya haifar da kwararan ‘yan mata daga Tunusiya da Aljeriya da Beljiyum da Faransa zuwa Siriya da Iraki domin su shiga cikin irin wadannan kungiyoyin na ‘yan ta’adda.

Ire iren labarun da wadancan matan suke fada dangane da yanda ake musu fyade da sunan jihadi da kuma sunan musulunci shine mafi bayyana daga cikin dalilan da ake bayarwa wurin amfani da matan wurin tabbatar da manufofinsu na kuskure kan ma’anar jihadi a musulunci domin masu karancin illimi da hankali daga matasan musulmai su shiga layinsu, a bisa wani kididdiga na Majalisar Dinkin Duniya da ta fitar ya nuna cewa kungiyar ISIS ta tilastawa matan aure da kanana ‘yan mata kusan 1500, tare da samari zama bayin zina “na’urorin biyan bukata” wanda wasu matanma an sayar dasu a matsayin bayi ko  bursunonin yaki.

Wannan ba karamin jarabawa bace ga dan adam, domin hakan ya shiga sahun ‘ Cinikin mutane” wanda kuma malaman fikihu sun tabbatar da haramcinsa, dukkan mutane – Bisa yarjejeniyar kasa da kasa mai kula da wannan lamari – masu ‘yanci ne, su ba kayan hajar sayarwa bane, hakika musulmai sun rattaba hannu akan yaejejeniyar kasa da kasa wacce ta tabbatar da kawo karshen kangin bauta ga mutane, domin hakan ya yi daidai da manufar musulunci na kuntata mabubbugansa da yalwata kofofin ‘yanci don mutane su kasance – Dukkansu – masu ‘yanci kamar yanda Allah Ta’ala ya haliccesu.

Share this:

Related Fatwas