Ƙungiyar ƴan’uwa na ƴan ta’adda ita...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ƙungiyar ƴan’uwa na ƴan ta’adda ita ce asalin ƙungiyoyi masu yaɗa zancen fitina, kuma asalin ƙungiyar Hawarijawa na zamani.

Tambaya

Shin me yasa ake ɗaukan Ƙungiyar ƴan’uwa na ƴan ta’adda matsayin asalin ƙungiyoyi masu yaɗa zancen fitina, kuma asalin ƙungiyar Hawarijawa na zamani?.

Amsa

Ta ɓangaren tunanin bai ɗaya, ko ta fuskar yin nazari ana la’akari ne da fahimtar wanda  ya assasa ƙungiyar wato Hassan al- Banna, da kuma littafan Sayyid Ƙuɗub wanda ya guntsa daga al-Banna da al-Maududi, fahimtar waɗannan na daga cikin al’amura da suke yi wa ƙungiyoyin ƴan ta’adda jagaora a gabashi da yammaci, musamman ma littafan nan guda Biyu wato: “Ma’alim fiɗ – Ɗariƙ”, da kuma “Fi Zilalil Ƙur’an”, ana kallon Hasan al-Banna da Sayyid Ƙuɗub a matsayin iyayen gijin waɗancan ƙungiyoyin a tarihinsu na wannan lokacin.

Amma ta fuskar tarihi, lallai ayyukan ta’addancin da ƙungiyar ƴan’uwa ta ƴan ta’adda suka yi shi ne laifin ta’addanci na farko da aka yi a wannan lokacin, a cikin shekarun 1940 na ƙarnin da ya gabata sun kashe firaministoci har guda biyu (2), da wani mai shari’a.

A shekarar 1950 kuwa sun yi ƙoƙarin kashe marigayi shugaban ƙasa Jamal Abdul –Naseer, kuma sun kusa yin nasara akan hakan, sannan suna da hannu dumu- dumu wurin kashe marigayi Muhammad Anwar As-sadaat.

Kuma idan aka lura za a ga da yawan waɗanda suka kafa ƙungiyoyin ta’addanci da mambobinsu suna da alaƙa mai ƙarfi da ƙungiyar ta’addanci na ƴan’uwa, misali Shukry Mustapha wanda ya kafa ƙungiyar (At-takfeer wal hijra), ya kasance suruki ne ga ɗaya daga cikin ƴan wannan ƙungiyar ta ƴan’uwa, an kama shi ne a shekarar 1965, tare da waɗanda aka kama su cikin ƴan ƙungiyar ƴan’uwa. Wannan duk ya kasance ne kafin ma ya kafa tasa ƙungiyar.

Share this:

Related Fatwas