Rashin bambance tsakanin abin da ya...

Egypt's Dar Al-Ifta

Rashin bambance tsakanin abin da yake asali ne da abin da yake reshe ne ɗaya ne daga cikin dalilan da suke sanya a tasirantu da fahimtar Hawarijawa masu tsattsauran ra’ayi

Tambaya

Mene ne ya sanya Rashin bambance tsakanin abin da yake asali da abin da yake reshe ya zama ɗaya daga cikin dalilan da suke sanya a tasirantu da fahimtar Hawarijawa masu tsattsauran ra’ayi?

Amsa

A cikin mafi munin sifofin Hawarijawa da suka saɓa wa Ahlus Sunna wal jama’a akwai sifar kafirta Musulmai idan suka aikata zunubi, muna nufin saɓani a cikin furu’a, shin wannan zunubin babban ne kaman barin salloli wajibai, ko cin abinci da rana a watan Ramalan, ko kuma yana cikin ƙananan zunubai, kaman sauraron giba, ko yi wa mutane limanci alhali ba sa sonsa. Ilimin Fiƙihu shi ne yake bincike da nazarin akan furu’a na addini, a wurin Ahlus Sunna wal jama’a ba a kafirta Musulmi sai idan an tabbatar da cewa ya saɓa wa asali daga cikin asalolin addini, kaman a ce ya yi inkarin kaɗaituwar Allah mai girma da buwaya, kuma alƙali ne yake da hurumin yin bincike domin tabbatar da wannan hukuncin, shi kuwa ilimin da yake bincike da nazari akan asalin addini shi ne Ilimin Aƙida, sai dai masu tsattsauran ra’ayi sun kwashin wasu mas’alolin furu’a sun jibga su a cikin mas’alolin asalin addini, kaman tawassuli da waliyyan Allah salihai, wanda wanna mustahabi ne, ko halal ne a wurin malaman manyan mazhabobi guda huɗu, haka ma masu tsattsauran ra’ayi ba su taƙaita na su saɓa wa jamhurin malamai, su ce tawassuli haramun ne ba alal misali, a’a kafirta duk wanda ya yi tawassuli da ɗaya daga cikin waliyyan Allah mai girma da buwaya suka yi! Saboda haka ne aka yi masu laƙabi da Hawarijawan zamani.

Share this:

Related Fatwas