Rashin fahimtar yanayin da ake ciki...

Egypt's Dar Al-Ifta

Rashin fahimtar yanayin da ake ciki da kyau shi ne babban bala’in da ya sami Musulmi a wannan zamani

Tambaya

Saboda mene ne ya sanya ake ɗaukan cewa: Rashin fahimtar yanayin da ake ciki da kyau shi ne babban bala’in da ya sami Musulmi a wannan zamani?

Amsa

Malamai sun bayyana cewa: lallai fatawa tana sauyawa daidai da sauyin lokaci da wuri, da yanayi da ma mutane, kalmar “al-waƙi’u” wato yanayi tana ƙunshe da waɗannan abubuwa guda huɗu, ta haɗa dukan abubuwan da suke na haƙiƙa ne da suka saɓa da abubuwan da aka hararo a hankali, akwai misalai masu yawa a cikin Hadisai da suke nuni zuwa ga irin yanda fatawar a Shari’ar Musulunci take tasirantuwa da yanayi, an ruwaito Hadisi daga Sayyiduna Abuhuraira cewa, wani mutum ya tambayi Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) game da rungumar iyali ga mai azumi, sai Annabi ya amince masa, wani ma ya zo ya yi irin wannan tambaya, Annabi ya hana shi, da aka lura sai aka ga wanda aka amince masan tsoho ne, wanda kuma aka hana shi kuma matashi ne [Abu Dawud]; saboda shi tsoho yana da ikon da zai yi wa sha’awarsa burki sama da matashi. Wannan sauyi da aka samu a cikin wannan fatawa ta Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) tana komawa ne zuwa ga sauyin yanayi, idan har mai bayar da fatawa bai fahimci yanayi da kyau ba, to lallai babu shakka zai yi kuskure a fatawarsa. A cikin sifofin da masu tsattsauran ra’ayi suka sifantu da su akwai rashin kyautata fahimtar yanayin da ake ciki, hasali ma ba su yarda da shi ba; kaman yanda suke riya cewa wai ma ya saɓa da shari’a! hakan sai ya sa su yi ƙoƙarin sauya yanayin da ake ciki saboda wai ya yi daidai da hukunce- hukuncen shari’a, lallai wannan abu ne da ya saɓa da manhajin Annabi mai daraja, inda yake sauya hukuncin shari’a saboda ya yi daidai da yanayin da ake ciki, ba akasi ba.

Share this:

Related Fatwas