Kamanin yanda jahadi FisabilillaHi yake a wannan zamani.
Tambaya
Shin ya kamannin jahadi FisabilillaHi yake a wannan zamani?
Amsa
Jahadi FisabilillaHi yana da kamanni na zamani wanda ya dace da sauyawar zamani da cigaban rayuwa, abu na farko da yake zama wajibi akan Musulmai a matsayinsu na al’umma: shi ne kare daularsu a duk lokacin da aka so kawo mata hari bisa kowani irin manufa, sannan cigaba da yin shiri da taimakekeniya da kimtsawa da tanajin kudi domin daukaka kalmar Allah domin tunkarar duk wata barazana da za ta iya tasowa, haka nan kulawa da kan iyaka da kafofin shiga da fita domin datse duk masu tunanin kawo hari, amma ta fuskar daidaikun mutane kuwa: to a gaskiyar magana bayyananiya bisa kamannin jahadi wurin daukaka kalmar Allah ita ce shiga aikin hidimtawa kasa, da sanin haka a matsayin wajibi ne na addini da kuma kishin kasa, ya wajaba mu gane haka sosai domin mu a yanzu da ma lokaci mai tsawo da ya shude, ba ma bukatar daukar dakarun sojojinmu zuwa wani gari daban wanda ba na Musulmai ba domin kiransu zuwa ga addinin Musulunci, bugu da kari akan haka shi ne damar da kowa yake da ita ta tafiye- tafiye zuwa kasashen waje karkashin ‘yancin kowa ya yi addinin da ya ga dama, ko bayyana ra’ayinsa tare da hana nuna bambancin wariya tsakanin mutane saboda addininsu ko kabilarsu, kusan a yanzu za mu iya cewa akwai tashoshin talabijin da kafofin yada labaru na zamani da suka kutsa ko’ina cikin fadin duniya, sai hakan ya sauya lamura ta inda isar da kalma ga ko’ina cikin duniya abu ne mai matukar sauki.