ISIS ƙungiya ce ta ta’addanci

Egypt's Dar Al-Ifta

ISIS ƙungiya ce ta ta’addanci

Tambaya

Shin ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) ƙungiya ce ta ta’addanci?

Amsa

Ƙungiyar da aka santa da sunan ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) ba wai suna cikin ƴan ta’adda waɗanda suke yaɗa fitina cikin mutane ba ne akwai, hasali ma ƙungiyoyin alama ce bayyananniya ta ta’addanci, kuma mabiyanta su misalai ne bayyanannu ga waɗanda kalmar "ta'addanci" ta tabbata a gare su bisa cikakkiyar maa’anarta, shin wane ne ɗan ta’adda idan har ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..) ba su zama ta ƴan ta’adda ba?. Haƙiƙa labaru sun yi ta jerin gwano zuwa gare mu, sannan abubuwa da yawa sun faru, sannan an samu cikakkun rubuce- rubuce da suka yi da hannayensu, suka rubuta da kansu ba wai an rubuta masu ba ne, ko akansu wanda hakan yake zama magana ta yankan shakku da babu buƙatar kokwanto akan cewa waɗannan mutanen su ne mafi dacewa da cancantar a kira su da sunan ƴan ta’adda, da suke yaɗa zancen mai tayar da fitina a wannan lokacin. Haƙiƙa sun kafirta Musulmai, sun halatta zubar da jini, kuma suka zubar da jinin. Sannan sun kekketa mutumcin Musulmai, sun kwashe masu dukiyoyi, saboda wai dukkan garuruwan da ba su yi masu biyayya ba, wai kafirai ne, -kamar yanda suke rayawa– sannan suka wajabtawa mabiyansu yin hijira zuwa inda suke da ƙarfi ko iko!

Kai ka ce Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana siffantasu ne a inda yake cewa:  (A ƙarshen zamani wasu jama’a masu ƙarancin shekaru za su fito, waɗanda tunaninsu na wawacin ne, suna furta kalmomin fiyayyen halitta, suna kuma karanta Alƙur’ani, amma ba ya wuce maƙogwaronsu, suna fita daga addini kaman yanda kibiya take fita daga baka, idan kun haɗu da su ku kashe su, domin akwai lada a wurin Allah ranar alƙiyama ga wanda duk ya kashe su) [al- Bukhari da Muslim].

Share this:

Related Fatwas