Bambancin tsakanin ma’anar kisa da ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambancin tsakanin ma’anar kisa da yaki a Musulunci.

Tambaya

Menene bambancin da ke tsakanin ma’anar kisa da yaki a Musulunci ?

Amsa

Akwai bambance- bambance masu yawa tsakanin ma’anar kisa, da kuma yaki a Musulunci, bambanci na farko shi ne: kalmar (yaki) tana nuni ne zuwa ga yin tarayya a aiki da musanya daga mutane masu yawa, akasin kalmar (kisa), ita kuwa ba ta nuna hakan. Abu na biyu kuwa shi ne manufar yaki a Musulunci shi ne karya lagon mai ta’addanci, tare da kare kai daga cutarwarsa, ba wai kashe shi ba wanda zai kai ga raba shi da rayuwarsa, ta iya yiwuwa a yayin gudanar da yaki a samu kisa, amma ba shi ne manufar yaki ba, a duk lokacin da aka kare kai daga ta’addancin mutum aka karya lagonsa koda kuwa ba ta hanyar yaki ba ne, to ya wajaba a dakatar da karawar nan take a shari’ance, daga cikin haka akwai fadin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) inda ya ce: (An umurce ni da na yaki mutanen..) [al- Bukhari da Muslim], to “fi’ili” wato aikin “in yaki...” yana nuni ne zuwa ga tarayya da musanyan aiki tsakanin sassa biyu, bangare na farko su ne: mushirikan Kuraishawa da wadanda suke kewaye da su cikin wadanda suka kai wa Musulmai hari, don haka (umirtu..) wato an umurce ni na nuni ne akan lamarin hakan ya kebanci Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ne, haka nan fadin Allah mai girma da daukaka: (Ku yaki wadanda suke yakanku saboda daukaka kalmar Allah, amma kar ku yi ta’addanci) [Al-Bakra: 190], abin nufi da umurni a nassin Hadisi shi ne (yakar masu ta’addanci har sai an karya lagon su), idan aka kare kai daga cutarwarsu, to Allah ya umurce mu a ita wannan ayar da ta gabata da mu kame daga yi musu ta’addanci.

Share this:

Related Fatwas