Karanta Alkur’ani ba tare da alwalla ba
Tambaya
Shin ya halatta a karanta Alkur’ani ba tare da alwalla ba?
Amsa
Shari’a ba ta hana wanda bai da alwalla karanta Alkur’ani ba, an dai so kada a tabi Alkur’ani –da yake rubuce a takarda- idan mutum ba shi da alwalla; saboda Allah mai girma ya ce: (Babu wadanda za su tabe shi sai masu tsarki) [al- Waki’a: 79], sabanin wanda yake a cikin kwamfuta ko wata da sauransu;shi idan an tabe shi ba tare da alwalla ba babu komai; domin hukunce- hukunce rubutaccen Alkur’ani ba su hawa kansa.
Allah shi ne masani