Ma’anar istiwa’i a cikin hakkin Allah Ta’ala
Tambaya
Menene ma’anar “istiwa’in Allah a kan Al’arshinsa?” a cikin zancensa Allah Ta’ala (Allah Mai Rahama ya daidaita a al’arshi) {Daha : 5}
Amsa
Yana daga cikin akida tabbatacciya a wurin musulmai cewa lallai shi Allah Ta’ala babu wani wuri da ke dauke da shi, kamar yanda lokaci baya iyakance ikonsa, saboda wuri da lokaci ababen halitta ne, Allah ya tsarkaka daga wani abu cikin halittunsa ya jibince shi, ai shi ne yake jibintar komai, to wannan fahimtar shi ne aka aminta da shi a tsakanin musulmai, ba wani mai inkari da yake inkarin hakan, domin kuwa ma’abota ilimi sun yi karin haske kamar haka : Allah ya kasance ba tare da an masa wuri ba, shi ya kasance a inda yake kafin samun wuri, sannan baya canzawa daga yanda ya kasance. Amma abin da ya zo daga nassoshin Al’kur’ani da Hadisai da ke nuni kan daukakan Allah Mai girma da Buwaya akan bayinsa shi ne ake nufi da haka shi ne : girman matsayi da daukaka da rinjaye da kuma karfin iko, saboda Allah Ta’ala abin tsarkakewa ne daga kamanceceniya da halittunsa, kuma siffofinsa Ta’ala ba irin na bayinsa bane, babu wata siffa ta Mahalicci da ta zama irin ta halittunsa dake da tawaya, ai shi Allah mai siffofi ne cikakku, tare da sunaye kyawawa, duk wani abu ya zo maka a tunani to Allah ya saba daga hakan, domin rashin iya riskan abu shima riska ne, kuma matsa bincike akan sanin hakikanin zatinsa shirka ne.
Hakika ancewa Yahaya bin Mu’az Al’Razi : Ka bamu labari akan Allah Madaukakin Sarki. Sai ya ce: Shi ne Allah makadaici, sai aka ce masa : To yaya ya kasance? Sai ya ce: Shi ne mai mulki da iko, sai akace masa : to ina yake ? sai ya ce: Yana madakata, sai mai tambayar ya ce: Amma ban tambayake akan haka ba? Sai ya ce: Abin da ba haka ba to siffa ce ta abin halitta, to abin da na fada shi ne siffar Allah.