Madogaran masu tsattsauran ra’ayi w...

Egypt's Dar Al-Ifta

Madogaran masu tsattsauran ra’ayi wurin kafirta mutane

Tambaya

Mene ne madogaran masu tsattsauran ra’ayi wurin kafirta mutane?

Amsa

Kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi sun aje al’amuran na zanniyya da ake da sabani akan su a matsayin al’amuran  da suke kasancewa na yankan shakku ne wato yakini, inda suka sanya ra’ayoyin wakilan kungiyoyinsu da zababbunsu suka zama tushe domin yi wa mutane hukunci da su, don haka suka musanta samuwar mazhabobi na fikihu, haka nan suka kutsa cikin bidi’antar da mutane tare da daukar ayyukansu da zantuttukansu a matsayin abu mafi muni, wanda hakan ya kai su ga fadada kafirta mutane  da gama garinsu da nassoshi na zanniyat da tawili da kuma dimuwa wanda ke nuna jahilcinsu da rashin sanin makaman aiki na binciken ilimi, sai ka ga irin wadannan mutanen- alal misali - suna kafirta musulmai saboda su na yin tawassuli da Annabi SallaLahu AlaiHi wa sallam, inda suke fuskantar Allah da matsayin Annabi SallaHu AlaiHi wasallam, duk fa da cewa hakan yazo cikin Hadisai masu daukaka, An samo daga gareshi Annabi SallaHu AlaiHi wa sallam, yayin da yake koyawa wani mutum cikin al’ummarsa addu’a bayan ya samu matsalar makancewa, sai ya zo wurin Annabi SallaHu AlaiHi wasallam sai yace: ka rokamin Allah ya bani lafiya, sai yace masa: (Idan kana so nayi maka addu’a, idan kuma ka na so ka yi hakuri domin shi yafi zama alheri gareka) sai mutumin yacewa Manzon Allah : Roka min Allah..Sai Annabi ya umurce shi da ya yi alwala, sai ya yi tare da kyautatawa sannan ya karanta wannan addu’ar : ( Ya Allah ni ina rokonka ina mai fuskanta zuwa gareka da Annabinka Muhammadu Annabin rahama, ni na kama kafa da kai zuwa ga Ubangijina akan biyan bukata wannan domin a biya mini ita, Ya Allah ka sanya cetonsa ya game dani), Tirmizi, sai Akibah yace: Wannan Hadisin ingantacce ne kuma Sahih ne, shin akwai mai iya cewa Annabi SallaHu AlaiHi wa sallam, ya koyawa al’ummarsa abin da bai halasta ba a shari’a ko wani abu da ke rusa tauhidi?

Share this:

Related Fatwas