Saba wa ijma’in malaman al’umma

Egypt's Dar Al-Ifta

Saba wa ijma’in malaman al’umma

Tambaya

Muna fatana a yi mana Karin bayani game da wasu mas’aloli da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suka keta ijma’in al’umma?

Amsa

Fita daga, da saba wa ijma’in al’umma daya ne daga cikin al’amurran da suke yi kamari a hankula da zukatan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da masu kafirta Musulmi, fara tun daga Hawarijawa har zuwa ga kungiyoyin da suka rungumi tashin hankali a wannan zamani, wadanda su din cigaba ne na kungiyar Hawarijawa, wannan ne abin da Hadisin da ya sifanta ya yi nuni, inda ya sifanta su da yawan ibada da ayiki, tare da rasa nagartaccen manhaji, an ruwaito Hadisi daga Zaidu Bn Wahbi al- Juhniy, cewa wata rana yana cikin rundunar da suke tare da Aliyu (Allah ya kara yarda da shi), wadanda suka tafi wurin Hawarijawa, sai Aliyu (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: Ya ku mutane, lallai na ji Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (wasu mutane za su bayyana daga cikin al’ummata, suna karanta Alkur’ani, karatunku a gaban karatunsu ba komai ba ne, sallarku idan aka gwama da sallarsu ba komai ba ne, haka ma azuminku idan aka gwada shi da azuminsu ba komai ba ne, suna karanta Alkur’ani suna zaton zai amfane su, amma akasin haka suke samu, sallarsu ba ta samar masu da lada ko daukakar daaja, suna fita daga Musulunci kamar yanda kibiya take fita daga baka) [Muslim].

Alamun wannan al’amari:

Wannan al’amari yana bayyana a cikin kungiyoyin zamani ta fuskoki da dama, a cikinsu akwai: yin amfani da manazartar da ta saba da manazartar Musulmai, inda z aka ga sun karkata wajen yin karatu a wurin wasu malamai banda wasu, hasali ma suna sukar wanda duk ya saba masu, wasun su kuma suna fahimtar magana sabanin manufarta, kawai saboda ta yi daidai da son zuciyarsu.

Haka ma suna jifan malaman Musulunci da cewa malaman gwamnati, suna sukar duk wani da ya rike mukami a hukumance a cikin kasa, saboda su dusashe darajarsa.

Suna kuma fadada tuhumar addinin mutane da bidi’a, suna cewa haka ya saba da daidai, idan kuma ka bincike duka mas’alolin da akansu ne suke jifan mutane da bidi’a, sai ka ga cewa malamai suna da maganganu kusan takwas, ko ma fin haka akansu, shin kuma kowane mabiyi yana bin muftinsa ne kaman yanda haka yake a tabbace, shi kuma mufti yana da daman ya zabi daya daga cikin maganganu mujtahidai wajen gyara ayyukan mukallafai, saboda kauce wa fada wa cikin saba wa shari’a, idan ya gina akan abin da ya bayyana masa na ka’idoji da sharuddan ta’amuli da nassoshin shari’a, hakan sai ya sanya ya rage jifan mutane da bidi’a; sabanin abin da yake faruwa daga kungiyoyin da suka rungumi tashin hankali a matsayin manhaji, wannan ya faru ne sakamakon suna da madogararsu ta kansu da bas a bin wasunsu, sun kuma kaurace wa abin da yake hannun malaman Musulunci a tsawon karnonin da suka shude.

Share this:

Related Fatwas