Shafa fatiha bayan addu’a
Tambaya
Mene ne hukuncin shafan fuska da hannu bayan kamala yin addu’a, domin akwai wadanda suke bayyana hakan a amtsayin bidi’a wacce ake kinta?
Amsa
Yana daga cikin sunnah daukaka hannaye biyu a lokacin yin addu’a, tare da shafan fuska da su bayan kammala yin addu’an bayan yin sallah ko a wajenta, akan wannan fahimtar jumhor din malamai suka tsaya akai.
Allah ya umurcemu da yin addu’a sannan ya yi mana alakawarin amsa mana, Allah Mai girma ya ce:(Sai Ubangijinku ya ce ku rokeni zan amsa muku) [Gafir:60], yana daga cikin sunnonin da ake son aikatawa a lokacin yin addu’a daga hannaye, sannan a ashafi fuska da su hannayen bayan kammala sallah ko a wajenta, akan wannan akayu ittifaki tare da halascinsa a wurin Hanafiyya da Shafi’iyya da Hanabila, saboda fadin Manzon Allah sallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam: (Idan za ku roki Allah to ku rokeshi da tafin hannuwanku, kada ku rokeshi da bayan hannunku, sannan ku shafa fusakunku da hannayenku) Hakeem.
 Arabic
 Englsh
 French
 Deutsch
 Urdu
 Pashto
 Swahili
