Hakimiyya

Egypt's Dar Al-Ifta

Hakimiyya

Tambaya

Masu tsattsauran ra’ayi suna riya ce Musulmai bas a hukunci da shari’ar Allah Madaukakin Sarki, hasali ma sun sauya ta ne da dokokin kafirai, mene ne hakikanin wannan magana?

Amsa

Hakimiyya a takaice tana nufin mutane su yi aiki da shari’ar Allah Madaukakin srki a cikin duk wani abu nasu da ya shafi mas’alolin addini da na duniya.

Babu shakka yin hukunci da abin da Allah ya saukar na shari’arsa yana cikin wajibai na kan gaba, farali na aini akan kowane Musulmi ya yi hukunci da abin da Allah ya shar’anta, ya kuma sallama masa ya yarda da shi.

Duk wannan ya amince da cewa shari’ar Musulunci ita ce asalin dukan dokoki, bai yi inkarin sanannun abubuwa na addini ba –kaman wajibcin sallah, da zakka da haramcin giya da sat aba alal misali- to lallai ya fita daga da’irar kafirci.

Sakin baki wajen kafirta duk wanda ya yi hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar Magana ce ta hawarijawa da wadanda suke yi kama da su wajen kafirta Musulmai da zato, ko son zuciya, ya kamata mu fadakar da cewa dukan dokokin da ake samarwa a kasashen Larabawa da na Musulmai domin a yi aiki da su a kotunan shari’ar Musulunci –bayan mun bi diddigi mun tabbatar da cewa: an yi la’akari da shari’ar Musulunci wajen samar da su, inda suke yin daidai da mafi rinjayen maganganun malamai masana Fikihu, ko wasu fahimtoci a cikin mazhabobi, koda kuwa wanda aka rinjaya ne, kuma an samar da dokokin ne bayan an lura da cewa ba su ci karo fa nassoshin shari’a ba, sannan sun yi daidai da maslahohin al’umma.

Share this:

Related Fatwas