Bayyanar tsattsauran ra’ayi
Tambaya
Ta yaya mai tsattsauran ra’ayi yake bayyana a cikin al’ummu?
Amsa
Shi dai mai tsattsauran ra’ayi ba ya bayyana a cikin al’umma a lokaci daya, maimakon hakan ya kan yi amfani da wasu dabaru ne masu yawa domin jan ra’ayin mabiya da magoya baya, a irin wannan yanayi ne za mu ga yana kokarin nuna kansa a matsayin mai kira zuwa ga Allah - a cikinsu – kuma kamar wani manzo da yake kokarin gyara lamuran duniya da kuma al’umma, kamar yanda zai kasance yana bayyana abin da ya yi amanna da shi a matsayin matakin warware dukkan wasu matsaloli na rayuwa kebabbu ko kuma na bai daya, amma daga karshe ana iya gano cewa mayaudari ne.
Hakika malamai da yawa masana halayyan dan adam da na zamantakewa sun yi nazari sosai musamman akan lamuran falsafar tsattsauran ra’ayi – wanda hakan ke zama cikin mafiya munin ayyukan ta’addanci – saboda hakan na zuwa ne sakamakon halayya munana da suke kalubalantar kyawawan dabi’u da halayyar da aka saba da su, wanda shi mai tsattsauran ra’ayi yake tasirantuwa da munanan halayyar don jagorantar mutane zuwa ga farfajiyarsu, irin wadannan munanan tunanin da suke naso a zukatan ‘yan ta’adda, suna tasowa ne sakamon nesantar juna da ke tsakaninsu da kuma al’ummun da suke rayuwa a cikinsu.
Babu shakka irin wancan halin na nesantan jama’a ballantana sanin matsalolinsu na dosuwa a zuciyar mai tsattsauran ra’ayi a hankali ne sakamakon wasu dalilai mabanbanta ko masu hade da juna, wanda sashen hakan yana komowa ne sakamakon rashin natsuwa da mai tsattsauran ra’ayin ke fama da shi, kamar jin cewa an mayar da shi saniyar ware, ko kuma ana nuna masa kyama, tare da son kadaici, duk wadannan abubuwan suna haifar masa da ta’assubanci da nuna son isa a zuciyarsa, shi mai tsattsauran ra’ayi mutum ne mai son nuna isa, kuma hakan yana bayyana ne ta fuskar ayyukansa bayan ya rungumi tunanin tsattsauran ra’ayi, sai ya zama ya amshi irin wannan mummunan ra’ayin saboda ya yi dai dai da irin tunaninsa.