Kwakwalwar mai tsattsauran ra’ayi
Tambaya
Wani abu ne mafi bayyana alamomi da suke da tasiri a kwakwalwar mai tsattsauran ra’ayi?
Amsa
kwakwalwar mai tsattsauran ra’ayi na siffantuwa da wadansu alamomi da suke yin tasiri wurin wayewar tunaninsa har zuwa ga matakin zama cikakken mai tsattsauran ra’ayi, mafi bayyanar wadannan alamomin sune:
mika wuya ga ma’abota tunani mai tsauri yakan kasance ne a gaba-gaba fiye da asalin abin da ya kanshi tunanin, don haka mika wuyan masu biyayya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda abun gabatarwa ne akan komai, kuma shi ne asali, yayin da mika wuya ga musulunci reshe ne ba tushe ba a wurinsu.
Danfaruwa da tunane-tunanen baya da tsarkakesu tare da nuna kiyayya ga duk wani abu sabo da banbance tsakanin kuskure da daidai dake dauke da su.
Manhajinsu na taho mugama ne tare da dukkan kungiyoyi da masu tunanunnuka da suka yi sabani da su a fahimta, shin wadancan kungiyoyin sun kasance na addini ne ko na jinsi ko na kabila ko kuma a a.
Toshe kafofin gaskiya: wanda hakan wata alama ce da ta ke bashi ikon canza gaskiya da shafe ta, tare da gabatar da dalilai da hujjoji wadanda suka yi hannun riga da yanayin da ake ciki.
Kulle kofofin tattaunawa da mutane tare da nuna rashin amincewa da duk wani ra’ayi wanda ya saba da nasu ko da kuwa shi ne gaskiya.
Rashin iya yiwa kai gyara, irin wannan halin shi ne yake sanya masu tsattsauran ra’ayi su kasance masu daskararren tunani wanda ba ya canzawa har abada daga baya, daga karshe sai su koma tsarkake jagororinsu da ke zama tarnaki ga amsar sabon tunani wanda yake da alfanu.
Rashin samun tunanin iya tattaunawa cikin sassauci, wanda hakan ke kaiwa ga karfafa ra’ayin kafirta mutane, kuma ya kara assasa hanyoyin zafafawa a cikin lamura bayan haka.