Fatawowin masu tsattsauran ra’ayi

Egypt's Dar Al-Ifta

Fatawowin masu tsattsauran ra’ayi

Tambaya

So da yawa masu kafirta mutane sukan saki fatawowi ba tare da yin nazari akansu ba ko kuma daidaito, muna bukatar yin tsokaci akan haka?

Amsa

Da yawa daga mutanen da ke kasancewa masu tsattsauran ra’ayi sukan fitar da fatawowi ba tare da sun mallaki mataki mafi karanci na sanin hakan ba, sukan yi amfani da haka ne domin yada fatawowi na zuga ayi barna tare da sake musu fasali a bakunansu, manufar hakan shi ne su samu damar aiwatar da tsanantawarsu ta hanyar fadada haramta abubuwa, babu shakka irin haka yana jefa su cikin matsaloli da yawa, daga cikinsu akwai:

Ta’assubanci da kafewa kan ra’ayi

Wato wannan daya ne daga cikin siffofin masu tsattsauran ra’ayi, inda za mu ga mai tsattsauran ra’ayi yana mayar da hankalinsa wurin kare ra’ayin da yake yin Imani da shi, kuma shi mai kafewa ne akan ra’ayinsa wanda rashin kwarewarsa ke bayyana a wurin mu’amala da sauran al’umma.

Karkata zuwa ga tunanin cewa duk wanda yake jayayya da su ko warware manufofinsu ashararai ne bisa halayyarsu.

Lallai abokin hamayya a wurin masu tsattsauran ra’ayi ba su kasance ba face mutanen banza, marasa halaye nigari, kuma marasa ikhlasi da amana, hakanan suna yi musu kallon kaskantattu wadanda suka cancanci a nuna musu kiyayya, kuma masu kekyashasshiyar zuciya da munin halaye, kuma su mutane ne marasa tsantseni, ko marasa takawa, ba wai kawai sun kasance ba sa tarayya da su bane a zantuttukansu da akidunsu da halayyarsu bane kawai, a’a kawai saboda suna yi musu kallon ne na daban ta hanya da ta saba da ta su kuma su suna da abubuwan da suka saba da nasu ko kuma suna kalubalantar juna.

Halayyar da take cin karo da juna tare da yawan jin damuwa:

Shi  mai tsattsauran ra’ayi yana kasancewa cikin fushi ne a koda yaushe, wanda hakan ne yake haifar masa da yanayi na damuwa mai cin karo da juna a mu’amalarsa da son zuciyarsa, ballatana kuma jin halin damuwa na koda yaushe da jin bacin rai wanda shi mai tsattsauran ra’ayi yake rayuwa a cikinsa, tare da fita daga tsarin zamantakewa na bai daya tare da tozarta tsarin zamantakewa da kyawawan halayyar da yake a cikin al’umma.

Share this:

Related Fatwas