Ma’anar neman madadi.
Tambaya
Mene ne ingantaccen ma’ana ta shari’a wurin neman madadi daga waliyai da salihai?
Amsa
Lallai ma’anar shari’a na neman madadi daga Annabawa da salihan bayi yana kasancewa sababi ne na amfana, kamar dai yanda wani daga cikinmu yake neman taimakon likita domin neman lafiya, anan babu dalilin yin tunanin cewa shi ne yake bayar da lafiyar a wannan yanayi ko kuma yana tasiri wurin yaye cutar, ai shi rawar da likita yake takawa shi ne neman agajinsa kawai ake yi a matsayin riko da sababi da tambayar ma’abota sani, haka nan su ma waliyai da salihai Allah ya sanya su ne sababi ne na shiryatar da mutane da inganta halayensu da tarbiyyantar da su, da kuma lura da abin da ke bayyane garesu ko yake boye har su fita daga jarabawar sabo na sarari da na boye, kamar dai yanda yazo cikn fadin Allah Ta’ala: (Sai suka bar zunubi na sarari da na boye)[An’aam:120], to su ne ma’abota sani da kwarewa cikin abin da Allah ya tsayar da su akai na yada kiran Allah da hidimta wa Musulmai a sarari da boye, babu bambanci a cikinsu tsakanin rayayyu da wadanda suka rasu, domin su ba su samar da amfani ko cutarwa daga kawunansu, kawai suna kasancewa ne dalilai daga Allah, neman madadi daga garesu – A zahiri – nema ne daga Allah kan ya karo mana madadi daga cikin abin da ya yiwa bayinsa waliyai da salihai baiwa da shi, kan Allah ya gudanar mana da alheri ta dalilinsu a hannunsu, domin girmamawa gare su kasancewarsu masoyansa kuma zababbun bayinsa saboda kusancinsu da shi, wannan shi ne abin da fahimtar Musulmai ya tafi akansa a da da yanzu daga cikin sahabbai da tabi’ai, daga baya sauran malamai masu aiki da iliminsu suka bi sahu, duk wanda ya ware daga wannan fahimtar ko ya musanta hakan to ba abin lura bane.