Halascin yin yabo da ibtihalat na bege
Tambaya
Mene ne hukuncin yabon Annabi Muhammad (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) da kuma ibtihalat na bege da kuma wakokin na addini?
Amsa
Yana daga cikin mafi girma da daukakan abin da bawa zai nuna soyayyarsa da Allah Mahaliccinsa, da kuma Manzonsa Mai girma: yin yabo da bege, saboda su din dalilai ne na nuna soyayya, tare da nuna gaskiya a cikin soyayyar, domin shi mutum aduk sanda yaso abu to yana yawaita yabonsa da ambatonsa, shi dai harshe baya bayyana komai face abin da ke cikin zuciya, kowani abu yana karuwa da yabo amma banda yabon Allah da Manzonsa, domin mai yabonsu ne ke samun daukaka, kai babu wanda ya cancanci a yabesa kamar Allah Ta’ala da Manzonsa Annabi Muhammad (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam), a cikin hadisin Al’aswad bin Sare’e - Allah ya kara masa yarda – ya ce: (Nace ya Manzon Allah na yabi Allah Ta’ala da wani yabo, sannan ya yabeka da wani yabo, sai ya ce: to fada muji, sai ya fara da yabon Allah Maigirma da Buwaya.) Imam Ahmad.