Tattauna abu a sanyawa jariri a aba...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tattauna abu a sanyawa jariri a abaki bayan haihuwa

Tambaya

Mene ne ma’anar tattauna abu a sanyawa yaro abaki bayan haihuwa wato “tahneek”?

Amsa

Shi dai “tahneek” wato tattauna wani abu mai zaki a sanyawa yaro a baki kamar dabino ko zuma ko kuma makamancin hakan a matakin farko sannan a sanyawa yaro jariri a baki, a kuma matse ruwan cikin bakin shi ake kida da tahnek, hakika malaman fikihu sunyi bayani akan haka inda suka tabbatar da sunnar haka da kuma nuna muhimmancinsa, saboda aikin Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam), an karbo daga Abu Musa Al-Ash’ary – Allah ya kara masa yarda – ya ce: (An haifa mini yaro sai nazo da shi wurin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) sai ya rada masa suna Ibrahim sannan ya jajjaga masa dabino a bakinsa). Anyi Ittifaki akansa.

Tare da lura da cewa duk wanda zai yi wannan aiki ya kasance kwararre ne akan hakan don gudun samun matsala, ya yin da ake neman gyara sai aga anyi barna.

Share this:

Related Fatwas