matsayin yin zikiri cikin jama’a
Tambaya
Mene ne hukuncin yin zikiri cikin jama’a
Amsa
Shi zikiri cikin jama’a abin shar’antawa ne da babu shubuha a cikin haka, ai mafi yawan ayoyin Alkur’ani ma sun yi umurni ne kan yin zikiri bisa umurnin Allah da sigar jam’i ne, kamar dai inda Allah Ta’ala yake cewa: (Ku ambaceni nima zan ambaceku) [Al-bakara:152], hakanan fadin Allah Ta’ala: (Kayi hakuri da kanka tare da wadanda suke ambaton Ubangijinsu da safe da yamma domin neman yardan Allah kada ka dauke kanka daga kansu) [Al-kahafi:27] tare da sauran ayoyi masu girma da suka yi nuni zuwa ga hakan da suke nuna shar’antar da haduwa domin ambaton Allah Ta’ala da kuma rokonsa, saboda haka wasu hadisan Annabi masu girma sun bibiyi juna, daga Abu Huraira Abu Sa’eed – Allah ya kara musu yarda – sun bayyana cewa sun shaida a wurin Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Wadansu mutane ba su taba zama sun ambaci Allah Mai girma da buwaya ba face Mala’iku sun kewayesu sannan rahama ta lullubesu kuma natsuwa ta gamesu sannan Allah yakan ambacesu a wurin wadanda suke madaukaka).