Yi wa Alkur’ani tawili na kimiyya

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa Alkur’ani tawili na kimiyya

Tambaya

Mene ne hukuncin mutum ya ce: ina son tawilin Alkur’ani mai girma a kimiyyance?

Amsa

Alkur’ani mai girma mu’ujiza ne na Allah Ubangiji da yake sabuntuwa a dukan zamunna, shi kuwa abin da ake nufi da tawilin Alkur’ani mai girma a fagen ilimi yana da ma’anoni masu yawa; idan abin da ake nufi shi ne fassara shi daidai da manhajoji da ka’idojin da ilimi yake la’akari da su; to ai wannan ne abin da Musulmai suka yi ta yi a tsawon zamunna, da kuma haka ne suka bayyana daidaito tsakanin littatafai guda biyu na Allah Madaukakin Sarki: wato littafin da ake kallo (halittu) da kuma wanda yake a rubuce (Alkur’ani).

Amma idan abin da ake nufi da yi wa Alkur’ani fassara ta ilimi shi ne sanya shi a wani manhaji da bai yi imani da gaibi ba, to wannan na nufin yin amfani da manhajin da ya saba da akida wajen ta’amuli tare da Alkur’ani mai girma.

Shi kuwa yin bincike a cikin ayoyin Alkur’ani mai girma, saboda a kara himma wajen binciken taskokin da suke kunshe a cikinsa a tsawon zamunna, da kafa hujja akan cewa lallai abubuwan da yake kunshe a cikinsa na ilimi suna ketarawa zuwa ga zamunna, kuma suna yin daidai da dukan zamunna, har da zamanin cigaban taknoloji, wannan abu ne da muke kira da kwadaitarwa akansa, idan abin ka’idojin da ake la’akari da su wajen ta’amuli da lafuzzansa da siyakin da ya zo da shi a wurin malaman Musulunci.

Abin da ya yadu da sunan “al- I’ijazul Ilmiy” kuwa yana dauke da daura lafuzza abubuwan da ba za su dauka ba a wasu lokuta, wannan abu ne da ba a so; saboda Alkur’ani littafi ne na shiriya da karantarwa, ba littafin kimiyya da fasaha ba ne, ire- iren wadannan abubuwa suna zuwa ne a matsayin ishara da nuni, bas u ake nufi bat un asali.

Share this:

Related Fatwas