Hukuncin yiwa mamaci talkini bayan ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin yiwa mamaci talkini bayan rufeshi.

Tambaya

Mene ne hukuncin lakkanawa mamaci tambayoyin da za ayi masa a kabari bayan an rufeshi?

Amsa

Yiwa mamaci talkini sunnar Annabi ce mai girma, domin tazo daga shugaban manzannai, kuma malaman hadisi sun karfafa wannan sunnar, kuma da yawan malaman al’umma da masana fikihunsu da suka biyo bayansu sunyi bayani kan halsacin hakan, domin cigaba da aiki da hakan ba tare da inkarin aikatawa ba, zancen cewa haramun ne tare da samun zunubi ga wanda ya aikata hakan kuntatawa ne ga abinda Allah ya yalwata.

Bai halasta ire-iren wadannan mas’alolin su rinka tayar da fitina da jayayya da raba kan musulmai ba, abinda ya kamata shine mu girmama sabanin dake tsakaninmu sannan muyi abinda aka saba gudanarwa kan lamarin.

Share this:

Related Fatwas