Hukuncin rashin yanka ragon suna.
Tambaya
Mene ne hukuncin barin yanka ragon suna ga wanda yake da ikon yankawa?
Amsa
Barin yanka ragon suna ga wanda yake da iko sakaci ne na samun lada mai yawa, tare da barin tasiri mai girma akan hakan, akika dai sunna ce mai karfi ta Annabi SallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam, kuma ya kwadaitar da ayi hakan, babu laifi a yankawa yaron da aka haifa akuya guda daya, kamar dai yanda mafi yawan malaman fikihu suka fada, hakan ya wadatar ga abin da aka haifa, shin namiji ne ko mace, domin haka Annabi SallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya aikata, saboda abin da aka ruwaito daga Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda, cewa Annabi SallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam, ya yanka wa Hasan da Husaini kowannen su rago guda-guda, Abu Daud.
Amma idan mutum ya yanka akuyoyi biyu ga namiji, ita kuma mace ya yanka mata akuya guda daya, to wannan shi yafi.