Hukuncin dasa kwalbon ido mai launi...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin dasa kwalbon ido mai launi.

Tambaya

Mene ne hukuncin dasa kwalbar ido mai laini ta hanyar yin aiki?

Amsa

Yin aiki domin sanya kwalba a cikin ido, wanda yake da launi abune da ya halasta, babu hani akan haka a shari’ance, shin wannan ya faru ne saboda magani  ko saboda inganta gani, ko kuma domin ado ne, amma kar ya kasance da niyyar yodara ne ko yin badda-kama,  kuma kar ya zama akwai cutarwa a cikin aikin da za a yi, a daidai lokacin da ake aikin ko anan gaba.

Share this:

Related Fatwas