Hukuncin bayar da zakkah ga dan’uwa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin bayar da zakkah ga dan’uwan da ake binsa bashi

Tambaya

Mene ne hukuncin bayar da zakkah ga dan’uwan da ake binsa bashi?

Amsa

Allah Ta’ala yana cewa: (Ita dai sadaka tana kasancewa ne ga talakawa da miskinai da kuma masu aikin tattarata da kuma wadanda ake kokarin jan ra’ayinsu hakanan wadanda suke cikin wurare da wadanda ake binsu bashi da wadanda suke daukaka aikin Allah da matafiyi to wannan umurni ne daga Allah) {Tauba:60} Hakika wannan Ayar ta bayyana yanda ya kamata a tafiyar da zakkah da rabata, sannan ta bayyana wadanda ake binsu bashi daga cikin wadanda suka cancanta a ba su zakkah, wato dai wadanda akwai bashin mutane akansu, kuma suka kasa biya.

Ya halasta a shari’ance mai bayar da zakkah ya baiwa dan’uwansa da ake bi bashi zakkarsa domin biyan abinda ake binsa na bashi, sannan ladan da mai zakkah zai samu anan ninki ne, saboda fadin SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Ita sadaka ga miskini lada daya ce ta sadaka, amma bayar da ita ga makusanci lada biyu ne, ladan sadaka da kuma ladan sada zumunci) Imam Ahmad.

Allah Subhanahu wa Ta’ala ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas