Karfafa yin bincike na ilimi.

Egypt's Dar Al-Ifta

Karfafa yin bincike na ilimi.

Tambaya

Mene ne hukuncin bayar da kudi akan bincike na ilimi na musamman akan mahalli daga cikin kudin zakkah?

Amsa

Kiyaye mahalli yana daga cikin raya kasa da ake nema cikin fadin Allah Ta’ala: (Shi ne wanda ya halicceku daga kasa sannan ya rayar daku a cikinta) [Huud: 61]

Hakika Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wa Sallam ya yi umurni da kiyaye abubuwan halitta da rashin lalatasu, Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wa Sallam yana cewa: (Babu wani musulmi da zai dasa wani abu na dasawa ko ya shuka wani abu na shukawa, sannan wani tsuntsu yaci abun ko wani mutum ko wata dabba face ya samu ladan sadakan wannan abun) Bukhari.

Shi musulmi ana bukatarsa da bin hanyoyin ilimi ne wurin raya kasa, wanda daga ciki akwai kiyaye mahalli tare da kalubalantar duk wani abu da zai cutar da mahallin ga al’umma.

Hakika Allah ya shar’anta zakkah ne domin ya kasance wani tsari ne na taimakon juna a tsakanin mutane, Allah Ta’ala ya ce: (Ita dai zakkah ana bayar da ita ne ga talakawa da miskinai da kuma masu aikin tattarawa da wadanda akeson jan ra’ayinsu zuwa ga musulunci da kuma wadanda suke neman fansan kansu da wadanda ake binsu bashi da wadanda suke daukaka kalmar Allah da kuma matafiyi wannan  farilla ne daga Allah domin shi Allah masani ne kuma mai hikima) [Tauba: 60] wato dai ita zakkah ga mutum ake fara gabatar da ita kafin mahallinsa, sannan aka sanya hanyar gudanarwar kudin (wurin daukaka kalmar Allah), masu bin diddigi daga cikin malamai sun bayyana cewa magudanar hakan jihadi zai shiga cikinsa, hakanan ilimi, saboda shi jihadi yana iya kasancewa ne da harshe, kamar yanda yake iya kasancewa da makami, don haka, tafiyar da kudin zakkah a bangaren binciken ilimi na musamman a sashen mahalli da kiyaye mahallin yana daga cikin abubuwa da suka halasta a shari’ance.

Share this:

Related Fatwas