Yi wa mamaci addu’a.
Tambaya
Shin ya halasta ayiwa mamaci addu’a cikin jumlar “Ya Allah ka sanya makomarsa ya kasance Aljanna”?
Amsa
Yin addu’a ga mamaci a cikin jumlar “Ya Allah ka sanya makomarsa ya kasance Aljanna” lamari ne da yake halas a shari’ance, yin amfani da k almar (makoma), hade da sunan Aljanna a cikin addu’a babu wani laifi a ciki, a bangaren shari’a ko a bangaren harshe.
Ba a lura da maganar wadanda suke bayyana cewa yin amfani da Kalmar (matsuguni) ko (matabbata) shi ne yafi dacewa da Aljanna ba (makoma) ba, wannan ba daidai bane ya kuma sabawa tsarin da Alkur’ani Maigirma ya zo da shi na amfani da kalmomi.