Addu’a a lokacin saukar ruwan sama

Egypt's Dar Al-Ifta

Addu’a a lokacin saukar ruwan sama

Tambaya

Shin ana amsar addu’a a lokacin saukar ruwan sama?

Amsa

Lallai addu’a a lokacin da ruwan sama yake sauka karbabbiya ce; domin lokaci ne na ni’ima da falala da baiwa daga Allah Ubangiji, da rahama daga gare shi zuwa ga bayinsa; k

aman yanda Hadisan Annabi masu daraja suka nuna, an ruwaito Hadisi daga Sahlu Bn Sa’ad (Allah ya kara yarda da shi), ya danganta wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa: (Abubuwa guda biyu ba a mayar da su: addu’a a lokacin kiran sallah, da lokacin da ruwan sama yake sauka) [Abu Dawud da al- Hakim].

An ruwaito Hadisi daga Abu Umama (Allah ya kara yarda da shi) daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ana bude kofofin sama, a kuma amsa addu’a a wurare hudu: lokacin da sahu za su hadu akan hanyar Allah, da lokacin saukar ruwan sama, da lokacin ikamar sallah, da lokacin hangen Ka’aba) [al- Baihakiy da al- Dabaraniy].

Share this:

Related Fatwas