Karanta suratul Kahfi ranar Jumu’a

Egypt's Dar Al-Ifta

Karanta suratul Kahfi ranar Jumu’a

Tambaya

Shin karanta suratul Kahfi a ranar Jumu’a yana daga cikin sunnoni?

Amsa

Shi dai karanta suratul Kahfi a kowani lokaci a ranar Jumu’a cikin yini da dare abu ne da ake so, ya halasta a karanta ta a boye ko a bayyane, tana daga cikin surorin da ake son karantasu a ranar Jumu’a, hakika ya zo daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa  Alihi wa Sallam cewa: (Duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar Jumu’a wani haske zai fito masa daga kasan kafarsa ya tashi har zuwa sararin samaniya ya rinka haskakashi a ranar alkiyama, kuma ana gafartawa wanda ya karanta surar na abin da yake tsakanin jumu’oi guda biyu) Baihaki.

Share this:

Related Fatwas