Isra’i da Mi’iraji

Egypt's Dar Al-Ifta

Isra’i da Mi’iraji

Tambaya

Mene ne abubuwan da suka faru a ya yin Isra’i da Mi’iraji?

Amsa

An yi isra’i da Annabi SallallaHu AlaiHi wa  Alihi wa Sallam a fadake, daga masallacin Makkah zuwa Masallacin Kudus, inda ya jagoranci sallah tare da Mala’iku da Annabawa, -Amincin Allah su tabbata a gare su- sannan sai aka tafi sama da shi  SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam a fadake daga Masdallacin Kudus zuwa “Sidratul Muntaha” sannan aka bujurowa da Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam a cikin wannan daren mai albarka yanayin da Aljanna take, domin yaga abin da Allah ya yi wa bayinsa nsgari tanajin ni’ima domin yi musu albishir, sannan kuma aka bijirowa da Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam da wuta, domin ya ga abin da Allah ya tanaza na azaba mai radadi domin ya yi wa kafirai da mushirikai gargadi da wutar, sai yaga abin da ya gani na daga cikin ayoyin Ubangijinsa masu girma, kamar dai surar Shugabanmu Mala’ika Jibril Alaihis Salam, kamar dai yanda Allah ya halicceshi, inda yake da fukafukai (600), haka nan ya ga kokoluwar sama da abin da ya lullubeta na daga cikin lamarin Allah, sannan yaga Ubangijinsa Mai girma da Buwaya kuru-kuru ba tare da kamanceceniya ko ta hanyar saduwar haske ba, sannan Allah Madaukakin Sarki ya yi Magana da shi ba tare da mai shiga Tsakani ko hijabi ba: (Sai Allah ya yi wa Bawansa wahayi da abin da ya yi nufi Zuciya ba ta karyata abin da ya gani ba) {Annjm:10-11}.

Hakika Allah Subhanahu wa Ta’ala ya farlantawa  Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam tare da al’ummarsa a cikin wannan daren mai albarka salloli guda biyar da za a rinkayi a cikin yini da dare, kowace sallah tana da ladan kashi goma: ana nufin ladan salloli hamsin salloli biyar suke da shi idan anyi, sai Allah ya kebance Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam da kyaututtuka wadanda babu wani cikin ‘yan’uwansa Annabawa – Amincin Allah ya tabbata a gare su – da ya rabauta dasu.

Akan wannan ne jumhorin  malaman fikihu da na Hadisi da masana salon zance suka tafi, kuma dalilai da hujjoji na shari’a masu inganci sun zo da yawan gaske akan haka. 

Share this:

Related Fatwas