Tsadar sadaki da tasirorinsa

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsadar sadaki da tasirorinsa

Tambaya

Mene ne hukuncin shari’a game da tsadar sadaki da kuma tasirinsa?

Amsa

Tsadar sadaki bas hi a cikin sunnonin Musulunci; saboda babban manufar yin aure shi ne kamewar samari da ‘yan mata, Annabi mai tsira da aminci yana cewa: (Macen da ta fi albarka, ita ce wadda ta fi saukin sadaki) [al- Hakim a cikin al- Mustadrak].

Dole ne a kaucewa yin tsada wajen sadaki, uba ya saukake sadakin ‘yarsa ta duk hanyar da zai iya, matukar ya sama mata miji na gari; saboda ku bayar da kariya ga matasanmu maza da mata ga barin bin karkatacciyar hanya, lallai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya gabatar mana da nasiha mai matukar muhimmanci a inda yake cewa: (Idan wanda kuka yarda da addininsa, da dabi’unsa ya zo neman auren ‘yarku, to ku aura masa, in kuma ba ku yi haka ba, to fitina da barna masu yawa ne za su kasance a bayan kasa) [al- Tirmiziy].

Share this:

Related Fatwas