Bambancin ilimin Falaki da ilimin T...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambancin ilimin Falaki da ilimin Taurari

Tambaya

Mene ne bambancin ilimin Falaki da ilimin Taurari?

Amsa

A shari'ar Musulunci babu abin da yake nuni zuwa ga haramcin ilimin Falaki, ko hana yinsa, saboda nassoshin da suke nuna zargin ilimin Taurari, duka sun ginu ne akan zato da kirdado da babu gaskiya a cikinsa, hasali ma cutar da mutane yake yi, shi kuwa ilimin Falaki a matsayinsa na ilimi bah aka yake ba; domin shi ilimi ne da yake da fagensa da malamansa, da kuma manhajin da ake karantarsa, karantarsa farali ne na kifaya, wanda idan aka rasa masu shi a cikin al'umma, to dukan al'umma ta yi laifi; kuma akwai maslahohi masu yawa na addini da na duniya a tattare da ilimin Falaki, ba a samunsu sai an karance shi.

Share this:

Related Fatwas