Yin sallah cikin sauri (Kwakkwafe)
Tambaya
Mene ne ma'aunin gaggawar da take tasiri a ingancin sallah?
Amsa
Gaggawar da take yin tasiri a ingancin sallah it ace: mai sallah ya gabatar da daya daga cikin rukunnai ba a natse ba, shi ne abin da malaman fikihu suke kira da samun natsuwa, ma'anar haka kuma shi ne dukan gabobi su sami natsuwa da tabbata na dan wani lokaci a lokacin da ake gabatar da dukan rukunnan sallah, kaman dai a ce lokacin da zai ishi mai ruku'i ya ce: (Subhana rabbiyal Azeem), mai sujada kuma ya ce: (Subhana rabbiyal A'ala) mafi karanci sau daya, idan ya gabatar da rukunin a cikin natsuwa da tabbatar gabobi, to wannan ya wadatar, idan sauri ya biyo bayan haka ba sauri ne da yake lalata ingancin sallah, ko ya bata dukan sallar ba.