Ka’idojin yanka dabbobi da tsuntsaye a shari’a
Tambaya
Shin yanka dabbobi da tsuntsaye yana da ka’idoji a shari’ar Musulunci?
Amsa
Yanka na shari’a shi ne: kammala fitar ran dabba ko tsuntsun da ake ci, ta hanyar yanke jijiyar jannaye, wanda shi ne magudanar jini, da makogoro, wanda shi ne magudanar abinci da abin sha, abin da ya fi nuna cika shi ne yanke manyan jijiyoyi guda biyu wadanda su ne suke kewaye da makogoro, ana kiran wannan abu da “zaka” watau tsarki; saboda halaccin da shari’a ta yi shi ne ya sanya yankar ta zama mai tsarki.
Sharadi ne mai yanka ya zama mai hankali, shin namiji ne ko mace, ya kuma zama Musulmi, ko Ahlul kitabi, abin da za a yi yanka da shi kuma ya zama mai kaifin da aka tanadar da shi domin yanka, kamar wuka da makamantan haka, ta yanda za ta yanke abin da ya wajaba a yanke na dabba ko tsuntsu cikin sauri, sunna ne a ambaci sunan Allah a lokacin yanka, a ce: “BismilLah Allahu Akbar”, ko abin da ya yi kama da haka.