Babban jahadi (Jahadul Akbar) da da...

Egypt's Dar Al-Ifta

Babban jahadi (Jahadul Akbar) da dangantakarsa da da ɗaukan makami

Tambaya

Mene ne babban jahadi? Shin ɗaukan makami yana ciki babban jahadi?

Amsa

Babu shakka akan cewa, babban maƙiyin ɗan Adam shi ne zuciyarsa, kuma yaƙarta shi ne babban jahadi, kaman yanda Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bayyana, lallai Allah yana shiryatar da wanda yake so zuwa ga hanya madaidaiciya.. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: (Duk wanda tãdarsa ita ce saɓa wa Manzon Allah (SallalLãhu alaiHi wa alihí wa sallam) bayan hanyar gaskiya da shiriya ta bayyana masa, ya kuma bi hanyar da ta saɓa wa hanyar da muminai suke bi, ya kuma miƙa al’amurransa a hannun maƙiyan muminai, to, kuwa za mu bar shi da abin da ya zaɓa, kuma da sannu Allah Maɗaukakin Sarki zai shigar da shi gidan wuta, lallai makoma irin wannan, makoma ce mai muni) [an- Nisa’i: 115], Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya ɗauki makami domin ya yaƙe mu ba shi a cikinmu..) [al- Bukhari da Muslim], haka ma ya sake cewa: (Musulmi ba zai gushe a cikin sauƙi da hutu a cikin al’amarin addininsa ba, matuƙar bai zubar da jini da Allah ya haramta a zubar ba) [al- Bukhari], lokacin da Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas (Allah ya ƙara yarda da su) ya je ya yi muƙabala da Hawarijawa, ce masu ya yi: “Yaya kuke gani idan na karanto maku bayyanannun ayoyi daga cikin littafin Allah, na kuma kawo maku wasu Hadisai daga cikin Sunnar Annabinsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) waɗanda ba za ku yi inkarinsu ba, shin za ku sauya ra’ayinku? Sai suka ce: Ƙwarai. Lokacin da ya bayyana masu, mutane dubu ashirin ne suka sauya ra’ayinsu, dubu huɗu daga cikinsu ne suka cigaba da riƙe ra’ayinsu, aka kashe su” [Abdurrazaƙ], babu abin da yake hana ɗan Adam bin gaskiya bayan ta bayyana masa, banda cutar da ta yi kane- kane a cikin zuciyarsa, irinsu: cutar girman- kai da hassada, ta farko ita ta ɓatar da shaiɗan, ta biyun kuma ita ce ta ɓatar da Yahudawan Madina a zamanin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).  

Share this:

Related Fatwas