Bambancin da yake tsakanin soyayyar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambancin da yake tsakanin soyayyar da ‘yan ta’adda suke iƙirari, da kuma soyayyar da ɗaukacin Musulmai suke yi wa Annabi Muhammadu Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Tambaya

Mene ne bambancin da yake tsakanin soyayyar da ‘yan ta’adda suke  iƙirari, da kuma soyayyar da ɗaukacin Musulmai suke yi wa Annabi Muhammadu Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi? 

Amsa

Ita soyayya dai manufa ce tare da samun karɓuwa daga ran mutum, da samun karkata zuciya, babban dalilin gaskiya da yake bayyana soyayya shi ne yin biyayya ga wanda ake so, kuma babu makawa sai an samu hakan a tabbace, a bisa waanan dalilin ne  wasu suka ce:

“Kana saɓa wa Allah sannan ka rinƙa bayyana sonsa, wannan yaudarar na rantse da Allah hankali ba zai ɗauka ba. Inda a ce soyayyarka gare shi da gaske ne, da ka yi masa biyayya. Lallai masoyi mai biyayya ne ga wanda yake so”.

Domin soyayyar da Musulmai suke yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) tana zuwa ne daga soyayyarsu da  suke yi wa Allah Maɗaukakin Sarki, Manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ku so Allah saboda abin da yake azurtaku da shi na ni’imominsa, sannan ku so ni saboda son Allah, sannan ku so iyalan gidana saboda soyayyar da kuke yi mini). [Tirmizi]. Musulmai ba su kasance suna kiyaye sunnar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da nuna wa iyalan gidansa soyayya da murnarsu na haihuwarsa, tare da farin cikinsu na yabonsa, da zaman majalisi na yi masa salati, da yin tawassali “kamun ƙafa’ da matsayinsa mai girma domin Allah Mai girma da Buwaya, da rausasawansu da ƙanƙantar da kansu ga sauran halittu ba, face sai don su bayyana irin soyayyarsu gare shi a aikace. Lallai akwai bambanci tsakanin irin wannan soyayyar da kuma soyayyar mutanen da suke haramta yin bukukuwan  maulidi, suke kuma hana zaman majalisin yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan ba sa yin farin ciki da yin yabonsa, kuma suke cewa yin tawassuli da matsayinsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) shirka ne, wai shin wannan wace irin soyayya ce suke rayawa kansu ita..?!

Share this:

Related Fatwas