Matakan da hanyoyin da idan muka bi su za mu kawo ƙarshe, ko dusashe tunanin Hawarijawa a cikin al’ummominmu
Tambaya
Waɗanne matakai da hanyoyi ne idan muka bi su za mu kawo ƙarshe, ko dusashe tunanin Hawarijawa a cikin al’ummominmu?
Amsa
Tunani irin na Hawarijawa yana ruguza al’umma, saboda tunani ne mai nuna ƙiyayya ga wayewa da gina ƙasashe, don haka wannan yana nuni kenan akan ci-baya da lalata abubuwa, kuma wannan tunanin lalatacce ne domin ya saɓawa ingantaccen fahimtar Alƙur’ani da Sunna, don haka babu makawa sai an bi hanyar tsaka-tsaki na gyara na inganci domin yaƙar mummunar tunanin Hawarijawa tare da yaye kallabin laifuffukansu, wannan kuwa shi ne yin kira zuwa ga Allah da hikima da kyakkyawan wa’azi, tare da yaɗa ɗabi’un daidaito da rangwame da kuma tsarin zaman tare, haka nan kuma da yin aiki tuƙuru wajen yin bayani domin gyaran fahimta da kuma saita munanan tunani, shin ga mabiya waɗannan ƙungiyoyi ne, ko kuma ga waɗanda aka ruɗe su suka shiga cikinsu, sannan kuma a yi aiki tuƙuru wajen gina kadarko na wayar da kan mutum don ya zama nagartacce, wanda ya yi daidai da tafarki na ilimi mai ƙarfi, wanda ya yi nesa da shaci faɗi, haka nan kuma hakan ya ƙunshi taimaka wa hukuma wajen cimma burinta na raya yankuna da samar da kayayyakin more rayuwa, saboda koma baya ta fuskar cigaba da raya yankuna da yaɗuwar cututtuka cikin al’umma kamar talauci, da rashin lafiya, da zaman kashe wando na daga cikin hanyoyin yaɗuwar munanan tunani.
Daga ƙarshe duk wanda ya riƙe makami yana kashe mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba, to fa ba shi da wani magani face a bi shi ta hanyar da ya zo, ai ta hanyar yi masa hukunci da kundin tsarin mulki da dokoki wanda mutanen da alhakin hakan ya rataya a wuyansu za su yi, wato zaratan rundunan sojoji mafi alheri a doron ƙasa.