Ƙoƙarin gwamnatin Misra wajen yaƙi ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ƙoƙarin gwamnatin Misra wajen yaƙi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi

Tambaya

Mene ne ƙoƙarin gwamnatin Misra wajen yaƙi da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi?

Amsa

Gwamnatin Misra tana iya ƙoƙarinta wajen yaƙi da ta ‘addanci da tsattsauran ra’ayi a dukan fagage da matakai, ta fagen tsaro lallai jami’an tsaron Misra suna gabatar da ayyukan da suka kamata, inda suke sanya ido, su kuma yi bibiya, su kuma daƙile duk wata hanya an ƙarfafa, da kuma kai hari na ba – zata, inda suke buga babban misali na sadaukarwa da jaruntaka da za su dawwama a ƙundin tarihi. A fagen zamantakewa kuma, ɓangarorin da abin ya shafa suna taimaka wa iyalan waɗanda hare- haren ta’addanci ya rutsa da su, ta hanyar kyautata rayuwarsu, da kuma ɗebe masu kewa, haka ma ana bayar da diyya ga dukan waɗanda suka yi asara sakamakon matakan da ake ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci. A fagen ilimi da tunani kuma cibiyoyin addini –musamman hukumar bayar da fatawa ta ƙasar Misra (Darul Ifta)- suna gabatar da ayyukansu na addini da kishin ƙasa yanda ya kamata, inda ta samar da cibiyoyin sanya ido da suke aiki wajen yaƙi da tsauraran fahimta da fatawowi, da kuma yaɗa nagartattun fahimta, da wayar da kai a tsakanin matasa, inda take amfani da dukan hanyoyi, musamman kafafen sadar da zumunta, da shafukan intanet, bayan tawagogi da shirye- shirye mabambanta na ilimi da da’aea, da shirya manyan tarurruka game da wannan al’amari.

Share this:

Related Fatwas