Hatsarin nesantar manhajin Al Azhar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hatsarin nesantar manhajin Al Azhar a rayuwar Musulmai da tasirin da hakan yake haifarwa

Tambaya

Mene ne hatsarin nesantar manhajin Al Azhar a rayuwar Musulmai da tasirin da hakan yake haifarwa?

Amsa

Ba wai wuce gona da iri ba ne idan muka ce: lallai nesanta manhajin Al Azhar da rayuwar Musulmai yana nufin kashe Musulunci a cikin zukatansu, da yaɗuwa ruɗu da sunan addini, hasali ma babba dalili na bayyana tsaurin ra’ayi da ta’addanci shi ne nasantar manhajin Al Azhar wajen karantar da addini da karantarsa da kuma kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki; saboda manhajin Al Azhar shi ne manhajin Ahlus Sunna wal jama’a, nesantarsa yana nufin nesanta manhajin Ahlus Sunna mai daraja, gwargwadon tangarɗar da aka samu wajen aiwatar da manhajin Al Azhar a rayuwar Musulmai, gwargwadon irin tangarɗar da za ta faru a addininsu, shi kuwa samun tangarɗa a addinin Musulmi, samun tangarɗa ne a rayuwarsa ta duniya da ta lahira, manhajin Al Azhar, ko kuma mu ce manhajin Ahlus Sunna ya ginu ne akan manyan ginshiƙai guda uku, ga su a jere: Aƙidar Ahlus Sunna wal jama’a (Aƙidar Asha’ira, da Maturidiyya, da Fudhala’ul Hanabila), da kuma bin ɗaya daga cikin mazhabobin Fiƙihu guda huɗu da ake bi (Hanafiyya, da Malikiyya, da Shafi’iyya, da Hanbaliyya), da Sufanci a matsayinsa na hanyar tarbiyyar zukata da tsarin rayuwa saboda Allah mai girma da ɗaukaka, akan wannan tsarin ne malamai magabata da waɗanda suka biyo bayansu suka kasance a tsawon lokaci har zuwa wannan zamanin, godiya ta tabbata ga Allah Unagijin talikai.

Share this:

Related Fatwas