Tsarkin wanda yake da lalurar fitsa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsarkin wanda yake da lalurar fitsari da kuma yin sallarsa.

Tambaya

Mai tambaya anan yana ganin wani sashe na fitsari yana diga bayan alwala da kuma lokacin sallah. Inda yake cewa: shin zai sake alola ne da sallah? Idan ya karanta Alkur’ani ba a cikin sallah ba sannan kuma digon fitsari ya zubo masa, shin zai kammala karatunsa ne?

Amsa

Shi tsarki sharadi ne daga cikin sharudan ingancin sallah, idan har fitsari ya fita koda kuwa digo daya ne ga mutumin da yake lafiyayya to alwalansa ta karye, saboda hadisin Abu Huraira Allah ya kara masa yarda cewa Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Allah ba ya amsar sallar dayanku idan ya fitar da hadasi har sai ya sake alwala) Bukhari.

Sai dai fa idan mutum ya kasance bashi da lafiya kuma fitsari yana yawan zuba masa ba tare da iya matseshi ba, to ya kamata ace ya yi alwala so daya kada ya damu da abinda yake zuba, kuma ana kallon sallarsa da karatunsa na Alkur’ani ingantacce ne, saboda wannan lalurar, alwalansa na warwarewa ne kawai idan wani abu da ya fita daga gareshi banda wannan lalurar.

Share this:

Related Fatwas