Watsi da harshen Larabci da karya ƙ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Watsi da harshen Larabci da karya ƙa’idojinsa ƙofa ce babba da tsaurin ra’ayi yake shigo wa ɗan Adam

Tambaya

Mene ne dalilin da ya sanya malaman Musulunci suke bai wa harshen Larabci kariya? Kuma saboda mene ne ake ganin cewa watsi da harshen Larabci da karya ƙa’idojinsa ƙofa ce babba da tsaurin ra’ayi yake shigo wa ɗan Adam?

Amsa

Harshen Larabci shi ne harshen da Allah ya saukar da Alƙur’ani mai girma da shi, da shi Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake magana, rashin sanin harshen yana nufin rashin sanin ma’anonin Alƙur’ani da Hadisai, da kuma kuskure wajen fahimtar manufar Allah ta halittar mutane. Lokacin da harsunan mutane suka yi rauni, aka fara yawaita yin kuskure wajen karatun Alƙur’ani, sai malaman Musulunci suka mayar da hankali wajen bai wa harshen Larabci muhimmanci, abin da ya kai su ga karkasa ilmomin da suke hidimta wa harshen Larabci zuwa kaso goma sha biyu, ko ma sama da haka. Akwai ayoyi da Hadisai da dama da idan mutum ya jahilci harshen Larabci da ma’anonin su to kuwa za su kai shi zuwa ga tsaurin ra’ayi, kamar maganar da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake cewa: (Umirtu an uƙátilan nasa hatta yashhadu allá Ilaha illalLah..) sanin ma’anar harafin ت da take nuni zuwa da mai aiki, da bambancin da yake tsakanin kalmomin (Aƙtulu) da (Uƙátilu), da sanin rukuni da nau’in da harafin ل da cikin kalmar (Annasa..) dukansu abubuwa me da za su sauya ma’anonin gaba ɗaya, daga nassin da yake halatta haƙƙin asali ga kowane ɗan Adam na ya kare kansa, zuwa nassin da yake dasa fahimtar tsaurin ra’ayi da ta’addanci..

Share this:

Related Fatwas