Watsin da masu tsattsauran ra’ayi s...

Egypt's Dar Al-Ifta

Watsin da masu tsattsauran ra’ayi suke yi da ilmomin hankali da Musulmai suka shigar a cikin ilmominsu, da dangantakar hakan da tsaurin ra’ayinsu da kuma rashin fahimtar addini da suka yi

Tambaya

Shin watsin da masu tsattsauran ra’ayi suke yi da ilmomin hankali da Musulmai suka shigar a cikin ilmominsu, yana da dangantaka da tsaurin ra’ayinsu da kuma rashin fahimtar addini da suka yi?

Amsa

Lallai watsi da ilmomin hankali da masu tsattsauran ra’ayi suka yi yana da babban tasiri wajen tsaurin ra’ayinsu, da ma rashin fahimtar addini da suke da shi, su ilmomin hankali, irinsu: ilimin Manɗiƙi, dokoki ne da suke kiyaye hankali kada ya yi tunani mara kyau, yin watsi da waɗannan ƙa’idoji shi ne yake haifar da kuskure da karkacewa wajen fahimtar Nassoshin Shari’a, da kuma fahimtar yanayin da ake ciki, duka biyun kuma suna da matuƙar muhimmanci wajen yin istinbaɗi daga hukuncin Shari’a, rashin fahimtar bambancin da yake tsakanin ɗabi’ar yanayin da nassi ya sauka akansa, da ɗabi’ar yanayin yanzu, shi ne yake kai wa zuwa ga ɓarnar tunani masu yawa, waɗanda hakan ne babban hanyar share fage ga tsauraran fahimta, kaman yanda malamai suka bayyana a cikin litattafan ilmomin hankali cewa: Yi ma abu hukunci wani sashe ne na yanda aka suranta shi, idan an suranta shi a kuskure, to hukuncin ma zai zama kuskure ne babu makawa, lallai malaman Musulmai sun yi aikin tace ilmomin hankali daga aibobin da yake cikinsa na tsawon ƙarnoni, sannan suka yi amfani da shi wajen ƙarfafa ginshiƙan ilmominsu, kaman yanda ya zo cewa: “Ita hikima abin neman mumini ne, a duk inda ya same ta da ma tashi ba”.

Share this:

Related Fatwas