Hatsarin da yake tattare da a ce ma...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hatsarin da yake tattare da a ce mai neman fatawa cikin gama- garin mutane ya nemi mufti da ya kawo masa dalili ko hujja

Tambaya

Mene ne hatsarin da yake tattare da a ce mai neman fatawa cikin gama- garin mutane ya nemi mufti da ya kawo masa dalili ko hujja?

Amsa

An hana mutum gama- gari da ba shi da ilimi mai zurfi a fannin Shari’a ya tambayi mufti dalili ko hujja akan fatawarsa; saboda shi mutum gama- gari ba shi da ilimin da zai ba shi daman duba zuwa ga dalili ko hujja, zai ma yiwu cewa ba zai fahimci dalilin ba, ko kuma ya fahimce shi ba ta fuskarsa ba, wannan kuma ɓata lokaci ne, da ɓata ƙoƙari, ko ma mu ce yaɗa jahilci, dukansu kuma abu ne da shari’a ba ta so, idan mai neman fatawa ya yi tambaya alal misali game da adadin raka’o’in Azuhur, mufti ya ce masa: huɗu ne, ya kuma tambaye shi hujja ko dalilinsa, sai ya ce masa: ijma’in malamai, mai neman fatawar zai buƙaci ya san mene ake nufi da ijma’in malamai? Yaya matsayin ijma’in malamai wajen kafa hujja? Kuma wane irin nau’in ijma’i ne wannan a cikin nau’o’in ijma’i da ake da su? Wannan kuwa ai darussa ne masu yawa da girma a cikin ilimin Usulul Fiƙihi, ba kuma kowa da kowa ne yake fahimtarsu ba, dole suna buƙatar shimfiɗu, saboda haka ne muka ga malamai tun da suka bayyana cewa sam bai kamata mai neman fatawa ya tambayin mufti y aba shi dalili ko hujja a fatawar da ya yi ba, sai dai idan yana son neman ilimi ne, koda kuwa gwargwadon da zai sami natsuwa ne, to yana da wannan daman, amma ba wai saboda ya amshi fatawar ko ya yi watsi da it aba.

Share this:

Related Fatwas