Ingantacciyar fahimta game da jahad...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ingantacciyar fahimta game da jahadi wurin daukaka kalmar Allah a Addinin Musulunci.

Tambaya

Ingantacciyar fahimta game da jahadi wurin daukaka kalmar Allah a Addinin Musulunci.

Amsa

Jahadi a cikin harshen Larabci kalma ce da take nuni akan “Abu mai wuya da matsa kaimi kan abu”, a shari’ance kuma Jahadi wurin daukaka kalmar Allah manufa ne da take da ma’ana mai yalwa. Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Wadanda suka yi jahadi saboda mu lallai za mu shiryatar da su zuwa ga tafarkinmu) [Al-ankabut: 69], malaman tafsiri sun ce: Abin nufi anan shi ne “Wadanda suka yi wa kawunansu jahadi wurin son zuciya da sha’awarta domin neman yardan Allah tare da neman shiriya, to lallai za mu shiryatar da su zuwa ga hanyoyinmu, haka nan ana tsinkayar da kalmar jahadi akan yakar abokanan gaba bisa manufar mayar da martani, ta kare kai daga ta’addancinsu, da kuma kare kai da kasa, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Ku fita baki dayanku samarinku da dattawanku sannan ku yi jahadi da dukiyoyinku da kawunanku saboda daukaka kalmar Allah) [At-tauba: 41]. To irin wannan jahadin daga cikin nau’ukan jahadi yana da nasa sharuddan na musamman, daga cikin akwai samuwar shugaba da neman izininsa, tare da samun tutar Musulunci bayyananniya, hakan samun kayan kariya da kimtsi, sannan tsara hakan ya rataya ne a wuyan shugabanni su kadai, don haka ne ma a cikin Musulunci aka ambaci haka da sunan “karamin jahadi”, hakika ya zo a cikin nassi cewa wasu mutane mayaka sun zo wurin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) sai ya ce musu: (Kun dawo daga mafi alhairin abin ake dawowa, daga karamin jahadi zuwa babban jahadi, sai suka ce: Mene ne babban jahadi? Sai ya ce: Bawa ya yaki son zuciyarsa) [al-Baihaki a babin zuhudul kabeer].

 

Share this:

Related Fatwas