Ingantaccen manhaji na daidaita bay...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ingantaccen manhaji na daidaita bayanai na Addini

Tambaya

Mene ne ake nufi da sabunta bayanai na Addini? Sannan mene ne Ingantaccen manhaji na daidaita bayanai na Addini?

Amsa

Abin da ake nufi da sabunta bayanai na Addini shi ne: komawa zuwa ga mabubbuga shari’ar Musulunci na asali, kuma kai tsaye, wato: Al’kur’ani Mai girma, da Sunnar Annabi mai tsarki, tsaftace bayanai na Addini daga abin da ya riske su a karshen zamani na wasu hanyoyin wayewa da wasu al’adu daban, da ba su da dangantaka da Addini ko kadan, misalin haka shi ne yi wa mata kallon kaskanci wanda ba na Musulunci ba ne, wanda hakan ya nauyaya wuyayen mace Musulma saboda tabaibayi da katanga da aka lika mata wanda ba a samu hakan daga Al’kur’ani ko Sunna ba, wata kila ma a samu tufka da warwara cikin lamarin da ya shafi mace kamar haramtawa mace fita domin yin aiki ko shiga harkokin siyasa da shiga sabgar zamantakewar al’umma, haka nan kuma lamarin da ya shafi dangantakar Musulmi da waninsa, wanda shi ma an samu kai- komo sosai na mummunar fahimta, saboda asalin dangantaka ta nesa a cikin Musulunci ita ce zamantakewa mai kyau da taimakekeniya, ba wai nuna kiyayya, ko kyama da yakar juna ba. Amma manhajin inganta bayani na addini mai kyau shi ne komowa zuwa ga Al’kur’ani Mai girma tare da daukarsa a matsayin littafi mai shiryarwa, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Ya ku mutane hakika hujja ta zo muku daga Ubangijinku sannan mun saukar muku da haske bayyananne) [An-nisa :174], yin tsinkaya zuwa ga sunnonin Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da ya shiryatar da mu zuwa gare su, kamar dai sunna daidaito, da sanayya, da bayar da kariya, ko cika- juna (takamuli), sannan sai abin da ya shafi manyan ka’aidoji, kamar dai al’amura da manufofinsu, sannan gusar da cuta, sannan kiyasta lalura da illarta, sannan kiyaye al’adun da aka saba rayuwa cikinsu, tare da yin aiki tukuru wurin kare manufofin shari’a wurin kare rayuka, da hankali, da addini, da dukiya, da mutumci, sannan karamar dan Adam.

Share this:

Related Fatwas